Ana shirye shiryen shigo da wasu ‘yan mata kasar nan domin yin karuwanci da kuma sayar da jarirai

0 384

Hukumar hana safarar mutane ta kasa NAPTIP ta an karar da jami’anta da kuma gwamnatin tarayya cewa yanzu haka ana shirye shiryen shigo da wasu ‘yan mata kasar nan kuma jihar Edo daga kasa Mali, domin yin karuwanci da kuma sayar da jarirai.

Babban kwamandan dake kula da shiyya ta biyu dake jihar Benin Barrister Nduka Nwawenene ne ya bayyana hakan a lokacin da suke tattakin yaki da safarar bil’ada da ake gudanarwa yau.

Taken bikin na bana, shi ne, aikin ceton wadanda akayi safarar su.

Ana bikin wannan rana ne domin hada karfi da karfe domin yakar wannan dabi’ar  musamman a tsakanin al’umma da kuma irin gudummawar da masu fada aji a cikin al’umma zasu bayar.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma bukaci al’umma suke bawa hukumomi hadin kai domin dakile matsalar a fadin duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: