Ana tuhumar mai dakin Ali Bongo da laifin karkatar da kudade da wasu laifuffuka

0 178

Ana tuhumar mai dakin hambararren shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, da laifin karkatar da kudade da wasu laifuffuka, wata guda bayan juyin mulkin da aka yi wa mijinta.

Sylvia Bongo Ondimba Valentin, wanda dan asalin kasar Gabon ne, kuma daya daga cikin ‘ya’yan ma’auratan ya zargi jagoran juyin mulkin da janyo cece-kuce a kasar mai arzikin man fetur.

Tuni dai aka tuhumi babban dansu Noureddin Bongo Valentin da laifin almundahana da almubazzaranci da dukiyar al’umma tare da wasu tsofaffin ‘yan majalisar da ministoci biyu.

A jiya ne alkali mai bincike ya tuhumi Sylvia Bongo tare da bayar da umarnin ci gaba da zama a gidan yari.

Haka kuma tana fuskantar wasu tuhume-tuhume da suka hada da boyewa da kuma jabu.

Ita dai Sylvia Bongo ta kasance a karkashin daurin talala a Libreville babban birnin kasar tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 30 ga watan Agusta.

An kebe ta da mijinta kuma lauyoyinta na Faransa sun shigar da kara a birnin Paris kan abin da suka ce da alama yin garkuwa ne.

Bongo, mai shekaru 64, wanda ya mulki kasar da ke tsakiyar Afirka tun shekara ta 2009, a ranar 30 ga watan Agusta ne shugabannin sojoji suka hambarar da su, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: