Gwamnatin tarayya na kokarin saka hannun jari a fannin hadin gwiwar hakumomin gwamnati da masu zaman kansu (PPP) a fannin kiwon lafiya domin tabbatar da samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.
Mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin kiwon lafiya, Dr Salma-Anas Ibrahim, ce ta bayyana hakan jiya a Abuja, yayin wata liyafar cin abinci da kungiyar masu ruwa da tsaki ta Kudancin Borno ta shirya domin karrama ta.
Dokta Salma-Anas ta ce manufar sabunta fata na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na daya daga cikin kudurin sa na inganta tsarin kula da lafiya domin cimma Maradun cigaba mai dorewa (SDGs).
Ta ce shugaban ya na da matukar kishin al’amuran mata da kananan yara, da kuma lafiyar ‘yan Nijeriya ya nada ta a matsayin mai ba shi shawara ta musamman.
Ko’odinetan cibiyar kasafin na Lafiya ta Afrika, Dakta Aminu Magashi, ya yi kira da a hada karfi da karfe tsakanin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, da hukumar kula da lafiya, da ma bangaren lafiya baki daya domin inganta ajendar kiwon lafiyar kasar nan.