Rundunar dakarun Operation Safe Haven, tawagar hadin guiwa dake aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato da rassan jihohin Bauchi da Kaduna, sun kama mutane 2 bisa zargin kisan wani mutum.
An bayar da rahotan yadda wasu yan bindiga suka bankawa wata cocin katolika wuta dake garin Kamaton a karamar hakumar Zangon Kataf a jihar Kaduna ranar 9 ga watan daya gabata, lamarin da yayi sanadin mutuwar wani mai ibada.
Da suka holan wadanda ake zargin shalkwatar rundunar, kakakin ta Captain Oya James ya bayyana sunayen wadanda ake zargi da suka hada Ahmed Abdullahi and Hassan Mato. Sai daya daga cikin su ya musanta zargin, inda yake bayyana cewa bai san komai akan abinda ake zargin sa da aikatawa ba.