Rikicin soyayya ya yi sandiyyar mutuwar wani matashi dan jami’a

0 273

An tabbatar da mutuwar dalibin aji biyu a fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa na jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma a jihar Katsina da aka bayyan sunan sa da Abubakar, biyo bayan wani rikicin dalibai akan budurwa.

Lamarin ya auku tsakanin dalibai 8 a  unguwar Darawa dake Karamar hakumar Dutsin Ma ranar alhamis.

Kakakin yan sandan jihar katsina ASP Abubakar Sadik a wata sanarwa daya fitar, yace takaddama ce ta faru tsakanin daliban, abinda ya kai ga mutuwar daya daga cikin su.

A cewar sanarwar kakakin yan sanda ya dauki lamarin da muhimmanci, kuma suna ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abinda ya faru. Kawo yanzu an kama mutane 6 bisa alaka da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: