Jagoran juyin mulkin Gabon na yin kokarin kawo karshen takunkumin da aka kakabawa kasar

0 284

Jagoran juyin mulkin kasar Gabon ya tattauna da shugaban kasar Congo Denis Sassou Nguesso a kokarinsa na kawo karshen takunkumin da aka kakabawa kasar.

Janar Brice Oligui Nguema ya ce ziyarar tasa jiya Lahadi a Congo-Brazzaville na da nufin karfafa alaka da makwabciyarta da kuma kawo karshen warewar da Gabon ke yi a yankin da ma duniya baki daya.

Hakan dai na zuwa ne makonni bayan da aka dakatar da Gabon daga cikin kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kungiyar kasashen tsakiyar Afirka Eccas bayan juyin mulkin ranar 30 ga watan Agusta. Kungiyar ECCAS ta kuma dauke shalkwatarta daga Gabon zuwa Equatorial Guinea bayan juyin mulkin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: