Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da tsaro ga manoman kasar nan

0 194

Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da tsaro yadda ya kamata domin kare Manoman daga hare Yan Boko Haram da na yan Bindiga da sauran tsageru domin su samu damar girbe aninda suka noma.

Wannan ya biyo bayan wani kuduri da dan majalisa mai wakiltar Chibok, Damboa da Gwoza Ahmed Jaha ya gabatar yayin zaman majalisar na jiya.

Da ya ke gabatar da kudirin, dan majalisar ya nuna damuwa dangane da yanayin tsaro a yankunan Chibok, Damboa da Gwoza, inda ya bayyana cewa mazauna yankunan na cikin tsoro lamarin dake hana su gudanar da harkokin noman su dama girbe abinda suka noma.

A cewar sa,lamarin na haifar da dimbin asara ga manoma da kuma samar da karancin abinci a yankunan dama kasa baki daya.

Yayi kira ga hukumomin tsaro da su samar da tsaro yadda ya kamata domin kare manoman yankin daga hare-hare yan ta’adda.

Shima dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da ta gabas a jihar Filato Dachung Musa Bagos, yayi kira da a samar da dokoki domin samar da tsaro ga manoma a kasa baki daya ba Chibi,Damboa da Gwoza kadai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: