Ana zargin cewa jam’iyyar APC ta fara tattaunawa da gwamnonin PDP guda uku

0 78

Ana zargin cewa jam’iyyar (APC) ta fara tattaunawa da gwamnonin jam’iyyar adawa ta (PDP) guda uku da niyyar dawo da su jam’iyyar mai mulki.

A cewar jaridar The Punch, kwamitin riko na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Mai Mala Buni ya fara tattaunawa da gwamnonin PDP uku wadanda suka hada da: Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwanyi na jihar Enugu da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

An  tattaro cewa majiyar ta kuma bayyana cewa tuni an kammala batun sauya shekar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: