Asusun yan fansho ya kammala biyan hakkokin iyalan ma’aikata 86 da suka mutu a bakin aiki

0 213

Asusun yan fansho na Gwamnatin jihar jigawa dana kananan hakumomin jiha yace ya kammala biyan dukkan hakkokin iyalan ma’aikata 86 da suka mutu a bakin aiki na sama da naira miliyan 292.

Babban sakataren asusun Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.

Yayi bayanin cewa, ma’aikata 577 da suka kammala shekaru 35 na aiki sun samu hakkokin su da suka tasamma sama da naira biliyan 1 da rabi na kudaden giratuti.

Alhaji Kamilu Aliyu Musa ka kuma kara da cewa iyalan yan fansho 38 da suka rasu kafin cika shekaru 5 da yin ritaya suma an biya su naira miliyan 33 da dubu 538 ta hannun magadansu. Kazalika Hakumar ta biya sama da naira biliyan 1 da miliyan 800 a matsayin hakkokin tsaffin ma’aikata sama da 700 da suka yi ritaya daga matakan aikin gwamnatin jiha da kananan hakumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: