Gwamnatin Jigawa ta godewa Alhaji Sule Lamido bisa bayar da gidansa daya ke ciki ga jami’ar jihar

0 125

Gwamnatin jihar Jigawa ta godewa tsohon gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido bisa bayar da gidansa daya ke ciki ga jami’ar jiha, domin mai dashi cibiyar nazari da binciken ilimin addinin musulunci.

Tawagar Gwamnatin jiha karkashin jagorancin sakataren gwamnati Alhaji Bala Ibrahim tace wannan karamci bai zo musu da mamaki ba, lura da soyayya da kishin jiha da tsohon gwamnan ke dashi.

Tun da farko tsohon gwamman ya bayar da sanarwar mallakawa jami’ar Sule Lamido dake kafin hausa gidansa na Bamaina bayan rasuwar sa domin mai dashi cibiyar.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan na musamman kan harkokin sabbin kafafen sadarwa Mansur Ahmad ya fitar a shafin sa na Facebook a yammacin jiya. Sule Lamido wanda ya mulki Jigawa tsakanin 2007 zuwa 2015 ne ya gina jami’ar lokacin da yake kan mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: