Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano na samar da na’urar mutum-mutumi

0 166

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, dake Wudil, wadda aka canjawa suna Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, na samar da na’urar mutum-mutumi da zai taimakwa ma’aikata wajen gudanar da ayyukan cikin gida kamar goge-goge, share-share da sauran kananan ayyuka a jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai, ya shaidawa manema labarai cewa na’urar mutum-mutumin za ta taimaka wa ma’aikatan wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya ce hukumar gudanarwar jami’ar ta samu ci gaba sosai a fannin fasahar kere-kere da amfani da fasahar sadarwa don baiwa dalibai damar yin amfani da fasahar gaba daya da kuma zama wani bangare na sauyin kirkirar fasahar sadarwa ta duniya.

Ya ce an riga an gwada na’urar robot din kuma tana aiki da kyau kamar yadda aka tsara. Ya kara da cewa jami’ar za ta samar da na’urori iri-iri da za su taimaka wajen rage yawan ayyukan da cibiyar ke yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: