Za’a dauki kwararan matakai kan mutanen da ke da hannu wajen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

0 111

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirin ta na daukar kwararan matakai a kan mutanen da ke da hannu wajen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin kasa, wanda ta bayyana hakan a matsayin babban laifi da ba za a iya cigaba da lamunta ba.

Ma’aikatar lura da harkokin ma’adanai ce ta bayyana hakan ne a yayin wani taro da masu lasisin hakar ma’adanai da kuma masu sana’ar kwasar yashi a jihar Kaduna, wanda aka gudanar domin magance kalubalen da ake fuskanta a fannin hakar ma’adinai.

Ministan lura harkokin ma’adanai Dr Dele Alake wanda mukaddashin jami’in yanki mai kula da ma’adanai na shiyya Kutman Ali ya wakilta ya jaddada muhimmancin bin hanyoyin bada lasisi. Ya bukaci ma’aikatan hakar ma’adanai dake jihar dasu yi kokarin biyan basussukan da gwamnati take bin su cikin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: