Ministan yada labarai ya ce cire tallafin man fetur shi ne mafi a’ala ga cigaban kasa

0 95

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, cire tallafin man fetur shi ne mafi a’ala ga cigaban kasa ta fuskokin bunkasar tattalin arziki da walwalar jama’a.

A cewar ministan, ba don gwamnati ta cire tallafin man ba, da wahalar da ake ciki a ƙasar sai ta fi ta yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.

Ana iya tuna cewa, a jawabinsa na farko bayan rantsuwar karbar mulki a watan Mayu na bara, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.

Tun daga wannan sanarwar ce kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta kara tsada ga jama’a.

Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanar da cire tallafin man fetur din farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: