An kama wasu mutane 6 da ake zargi da safarar man fetur ba bisa ka’ida ba a jihar Akwa Ibom

0 137

Hukumar bayarda tsaro ga farin kaya a jihar Akwa Ibom ta kama wasu mutane shida da ake zargi da safarar man fetur ba bisa ka’ida ba da kuma fasa bututu.

Kwamandan hukumar Mista Eluyemi Eluwade, wanda ya yi jawabi ga taron manema labarai a jiya Laraba a Uyo, ya ce jami’an hukumar da ke yaki da ayukkan ta’addanci sun kama wadanda ake zargin a kan babbar hanyar Calabar zuwa Itu a ranar 29 ga watan Janairu.

Ya ce rundunar ta kuma kama wata motar da wadanda ake zargin ke amfani da ita wajen kai haramtaccen man da kuma motar da aka yi amfani da ita a matsayin rakiya.

Kwamandan hukumar ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi shiga irin ta wata rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro kuma an same su da wata babbar mota dauke da man dizal da yakai kimanin lita 45. Ya lissafa wadanda aka kama sun hada da Abbas Ohis, Jubrin James, Aniefiok Okon, Maduka Ojukwu, Idorenyin Etim, da Uche Ahechukwu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: