AU ta dakatar da kasar Gabon daga shiga harkokin kungiyar bayan juyin mulkin sojoji na ranar laraba

0 225

Kungiyar tarayyar Afika AU ta dakatar da kasar Gabon daga shiga harkokin kungiyar bayan juyin mulkin sojoji na ranar laraba, lamarin da kungiyar tayi Allah wadai da shi.

Matakin ya biyo bayan zaman majalisar tsaro da kungiyar tayi a jiya Alhamis.

Tunda da farko dai wanda sukayi juyin mulki a Gabon sun sanar da soke sakamakon zaben da shugaba Ali Bongo yayi nasara.

Kawo yanzu dai sojojin basu sanar da lokacin mayar da mulki ga farar hula ba a kasar.

Jam’iyya mai mulki a kasar ta bukaci tattaunawa da jagororin juyin mulki a kasar domin samun mafita. Bugu da kari, yan kasar ta Gabon sun nuna farin cikin su dangane da kifar da gwamnatin Ali Bongo,amma kuma sunyi kira ga sojojin suyi mulki da adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: