Za’a tantance ma’aikatan gwamnatin jihar Jigawa daga ranar 4 – 30 ga watan satumbar nan

0 268

Gwamnatin Jihar Jigawa zata tantance ma’aikatan Gwamnatin jiha da na kananan hukumomi da kuma na sassan ilimi dake kananan hukumomi.

Kwamishiniyar kudi ta jiha, Furofesa Hannatu Sabo Muhammad ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta bayar.

Ta ce za’a gudanar da aikin tantance ma’aikatan ne karkashin kulawar ma’aikatar ta.

Furofesa Hannatu Sabo Muhammad ta bayyana cewa za’a gudanar da aikin daki-daki, inda za’a fara da ma’aikatu da hukumomin Gwamnati daga ranar hudu zuwa goma sha biyar ga watan Satumba, yayin da za’a gudanar da na ma’aikatan kananan hukumomi da na sassan ilimi a ranakun 18 zuwa 30 ga watan Satumba.

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka aikewa ma’aikatu da hukumomin gwamnati ranaku da kuma wuraren da za’a gudanar tantancewar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: