Babu wanda zai tsira, hatta da tsoffin gwamnoni – Shugaban EFCC

0 198

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede ya ce yaki da cin hanci da rashawa da ya ke jagoranta bai mayar da hankali kan masu damfara ta yanar gizo kadai ba.

Olukoyede, wanda ya yi magana a Abuja ranar Lahadi a wajen wani taron yaki da cin hanci da rashawa, ya ce babu wanda zai tsira, hatta da tsoffin gwamnoni.

Shugaban na EFCC ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa yakin da hukumar keyi zai ci gaba da fadada, kuma ba zasu kyale duk wanda suka kama da wani nau’i na laifukan tattalin arziki da kudi. Ya kuma gargadi matasa da su guji aikata laifukan da suka shafi yanar gizo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: