Bana zawarcin kujerar shugaban kasa, a cewar Farfesa Osinbajo

0 112

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya karyata labarin dake cewa yana daga cikin masu zawarcin Kujerar Shugaban Kasa a shekarar 2023.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakinsa Mista Laolu Akande ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, Farfesa Yemi Osinbajo, yana aiki ne tukuru a matsayinsa na mataimakin shugaban Kasa, domin magance matsalolin da suke addabar kasar nan, musamman fannin tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

Sanarwar ta ce Mista Osinbajo, bashi da masaniya kan hotunan sa na neman Takarar shugabancin Kasa a shekarar 2023 da ake kafewa a titina da kuma yadawa a kafafen sadarwa na zamani.

Masu sharshi suna ganin cewa ya kamata Mista Osinbajo ya tsaya Takarar shugaban kasa a 2023, sai dai Kakakin nasa ya bukaci mutane su dakatar da kiraye-kirayen.

Farfesa Osinbajo, shine wanda yayiwa shugaban Kasa Muhammadu Buhari takarar mataimakinsa a shekarar 2015 da 2019 a Jam’iyar su ta APC.

Kazalika, a shekarar 2023 ne wa’adin su zai kare, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: