Baza mu lamunci duk wani nau’in taruwar jama’a da sunan zanga-zanga ko tada zaune tsaye ba a jihar Kano

0 173

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da cewa zata samarwa mazauna jihar tsaro da zaman lafiya, kafin da kuma bayan sanar da hukuncin zaben gwamnan Jihar.

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Usaini Gumel ya sanarwa manema labarai cewa sun aike da isassun jami’an tsaro zuwa kwaryar birnin Kano.

Yace,bayan sanar da hukuncin zaben gwamnan ‘Yan Jihar suna da damar da zasu gudanar da murna, amma a gidajen su.

Kwamishinan ‘Yan sandan yace baza su laminci duk wani nau’in taruwan jama’a da sunan zanga-zanga ko tada zaune tsaye ba.

Usaini Gumel yace rundunar ‘Yan sandan Jihar, hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro a jihar bazasu bada damar kawo cikas ga zaman lafiyan jihar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: