Afrika ta Kudu ta kai gwamnatin Isra’ila kara gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC

0 332

Shugaban Cyril Ramaphosa, yace Afrika ta Kudu ta kai gwamnatin Isra’ila kara gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC bisa kisan kiyashi da take cigaba da yi a zirin Gaza.

Shugaban Cyril Ramaphosa yace la’akari da aikata laifukan yaki hakan yasa suka kai kasar kara gaban kotun ICC.

Ya kara da cewa basu goyi bayan harin da kungiyas Hamas ta kaiwa Isra’ila tunda farko ba, amma matakin da Isra’ila ta dauka ya wuce gona da iri.

Yana fatan kuma kotun hukunta Manyan laifuka ta kasa da kasa ICC zata yi bincike.

Kotun ICC dai kotu ce ta kasa da kasa da ke bincike kan laifukan yaki da kisan gilla a fadin duniya.

Gwamnatin Afrika ta Kudu na daya daga cikin kasashe dake goyan bayan Falasdinawa a yaki da take da Isra’ila. Wasu shugabannin kasashen sun nuna goyan su ga Falasdinawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: