Gwamnatin tarayya ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, a gaban kuliya, a kan tuhume-tuhume shida da suka shafi almundaha kan sayen wasu kadarori.
Daga cikin tuhume-tuhunen guda 20 na wasu kudade Naira biliyan 6 da milyan dubu 5, an rage shi zuwa shida, sai kuma Naira biliyan 1 da milyan dari 6.
A yau ne tsohon gwamnan na CBN ya gurfana a gaban kotu domin neman a bada belinsa, inda ya ki amsa tuhumar da ake masa na laifuka shida bayan karanta masa kunshin tuhumar.
A cewar takardar karar da aka yi wa kwaskwarima, har yanzu tuhume-tuhumen sun shafi almundahana kan wasu makudan kudade.
A cikin takardar da aka yi wa kwaskwarima, Gwamnatin Tarayya ta yi zargin cewa Emefiele ya sayi motoci 43 ba bisa ka’ida ba tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 na Naira biliyan 1 da milyan dari 2.
An zarge shi da bayar da kwangilar siyan Motoci kirar Toyota Hilux guda 37 da kudinsu ya kai Naira miliyan 854. An kuma zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa sabanin sashe na 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka na shekarar 2000 ta hanyar bayar da kwangilar samar da mota kirar Toyota Landcruiser V8 a shekarar 2019 kan kudi Naira miliyan 73.