Boko Haram sama da 200,000 ne suka ajiye makamansu tun bayan kaddamar da shirin yin afuwa a jihar

0 106

Gwamnatin Jihar Borno, ta ce akalla mayakan Boko Haram sama da 200,000 ne suka ajiye makamansu tun bayan kaddamar da shirinyjn afuwa a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Baba Sheikh ya shaida wa manema labarai wannan nasarar da suka samu a ziyarar aikin da ya kai Legas.

Ya ce gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya gayyaci duk masu ruwa da tsaki a Borno domin tattauna yadda za a kaddamar da shirin bai wa mayakan damar dawowa cikin al’umma.

Ya ce bayan samun amincewar shugabannin al’ummomin jihar, gwamnati ta kaddamar da shirin na kwance damara da sauya tunanin mayakan da kuma sake mayar da su cikin al’umma. A cewarsa tuni shirin ya samu karbuwa da kuma goyon bayan Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres wanda ya ziyarci jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: