An kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a jihar Adamawa

0 150

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, tare da kwato babur din da ake zargin sun karbo daga hannun wani Nuhu Muhammad.

Manema labarai sun ruwaito cewa hakan ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da aka kaiwa wani Nuhu Muhammed hari a kan gadar Jimeta a babban birnin jihar, Yola.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya fitar, ya bayyana sunayen ‘yan fashin da ake zargin Abdullahi Yusuf mai shekaru 22 da da Umar Yahaya mai shekaru 20.

Sauran biyun kuma su ne Hassan Ishaka mai shekaru 24 da Shuaibu Abubakar mai shekaru 19. An dai bayyana dukkan wadanda ake zargin da mazauna kauyen Kwabura ne a karamar hukumar Hawal ta jihar Borno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: