Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen zazzafar rana da kuma tsawa daga yau Litinin zuwa ranar Laraba.
Hasashen yanayin da Hukumar NiMet ta fitar jiya Lahadi a Abuja ya yi hasashen yanayi mai tsananin rana a sassan jihohin Yobe da Borno a yau Litinin, tare da yiwuwar tsawa a wani bangare na Kebbi.
A cewar NiMet, sauran sassan Arewa zasu su kasance cikin rana tare da gajimare a lokutan safiya. A wannan rana, ana sa ran za a yi rana a wasu sassan jihohin Bauchi, Taraba, da Kaduna.