Hukumar NDLEA a jihar Kano ta kama mutane 319 tare da kama tan 4.7 na haramtattun kwayoyi

0 105

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano ta kama mutane 319 tare da kama tan 4.7 na haramtattun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2024 a jihar.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Abubakar Idris-Ahmad ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a yau Litinin a Kano.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da mata 14 da maza 305.

Idris-Ahmad ya ce jimillar magungunan da aka kama a cikin tsawon lokacin da ake binciken sun haura tan hudu na haramtattun kwayoyi, wanda ya kunshi kilogiram 2.3 na tabar wiwi da kuma kilo 2.4 na abubuwan da suke lalata kwakwalwa.

Ya ce jami’ansu sun kuma kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan biyar da kuma kilo giram 1.9 na wasu abubuwa masu hadari. A cewarsa, a cikin watanni ukun, rundunar ta kama wasu mutane 33 da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi da sauran laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: