An samar da akalla jami’ai 951 na hukumar bada tsaro ga farin kaya don gudanar da bikin sallah a Anambra

0 102

Rundunar bada tsaro ga farin kaya ta kasa reshen jihar Anambra, ta ce ta tura akalla jami’ai 951 don kare muhimman kadarorin kasa da wuraren ibada a fadin jihar a yayin bikin karamar sallah.

Kwamandan hukumar na jihar, Maku Olatunde, ne ya bayyana hakan inda yace wannan wani mataki ne na dakile ‘ayukkan ta’addanci a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.

Ya bayyana hakan ne a garin Awka a yau Litinin yayin da yake bada umarni ga dukkan kwamandojin yankin da su tabbatar da samarda tsaro da kuma ganin an gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana.

Kwamandan hukumar ya kuma bukaci mazauna jihar da su kasance masu lura, da bin shawarwarin tsaro tare da hada kai da hukumar tasu da sauran jami’an tsaro domin dakile duk wani rashin zaman lafiya a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: