Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya bayyana cewa cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 13 a bara.
Ya ce wannan ya samar da ayyuka ga ‘yan Najeriya da Amurka tare da bunkasa dangantakar kasuwanci.
Mills ya ce sun kaddamar da sabon shiri na CIP domin saukaka harkokin kasuwanci tsakanin kamfanonin Najeriya da Amurka. Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya da Amurka na da tarihi mai karfi na fahimtar juna da hadin gwiwa.