Gwamnatin Jigawa ta umarci malamai 244 da suka bar aiki ba tare da izini ba da su mayar da albashin da suka karɓa ko su koma bakin aiki

0 748

Gwamnatin Jihar Jigawa ta umarci malamai 244 da suka bar aiki ba tare da izini ba da su mayar da albashin da suka karɓa ko su koma bakin aiki.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB), Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan halin da waɗanda abin ya shafa ke ciki.

Ya ce waɗannan malamai sun daina zuwa makaranta na tsawon watanni, amma suna ci gaba da karɓar albashi. Wasu daga cikinsu ma sun ɗauki wasu mutanen da ba su da ilimin koyarwa domin su riƙa maye gurbinsu, sannan su riƙa ba su ₦5,000 ko ₦10,000 ko ₦20,000 a kowane wata.

Ya ce: “Abin takaici ne yadda wasu malamai ke ci gaba da bata kokarin gwamnati na yaki da matsalar yara marasa zuwa makaranta, kuma gwamnatin ba za ta lamunci hakan ba.”

Leave a Reply