Majalisar Dattawa ta binciki hukumar ICPC kan yadda take bin dokar wakilci na shiyyoyi a tsarin daukar ma’aikata
Majalisar dattawa ta binciki hukumar ICPC kan yadda take bin dokar wakilci na shiyyoyi a tsarin daukar ma’aikata.
Shugaban hukumar, Musa Aliyu, ya bayyana cewa ma’aikatan ICPC sun kai 1,163, inda yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma suka fi yawan wakilci.
Ya ce an rarraba mukaman manyan daraktoci daidai gwargwado a shiyyoyi shida. Sanatoci sun yaba da gaskiyar ICPC tare da bukatar sauran hukumomi su yi koyi.