Shugaba Tinubu ya kaddamar da cibiyar masana’antar dijital ta Arewa maso Yamma da ke jihar Kano

0 139

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da cibiyar masana’antar dijital ta Arewa maso Yamma da ke Kano bayan an gyara ta daga lalacewar da ta samu a 2024.

Ministan sadarwa, Bosun Tijjani, ya bayyana cewa cibiyar za ta taimakawa matasa dubu 180,000 da kwarewar zamani da za su inganta rayuwarsu.

Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta ta horas da matasa dubu 300,000 kafin 2027, yayin da aka ba ministan sarautar “Sarkin Yakin Digitalization na Kano”. An bayyana cewa cibiyar na daga cikin burin gwamnatin Tinubu na samar da hazaka miliyan uku a fannin fasahar zamani.

Leave a Reply