Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji daga Arewa maso Yamma sun kashe ‘yan ta’adda hudu a jihar Zamfara a wani samamen hadin gwiwa.
An gudanar da samamen ne a wasu maboyar ‘yan ta’addan a kauyukan Tazame, da Mashema, da Gandaya, da Maje, da kuma Doka da dajin da ke kusa da kauyen Gandaya na karamar hukumar Bungudu.
Kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ Kyaftin Yahaya Ibrahim shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, inda ya ce wasu ‘yan ta’adda da ba a tabbatar da adadinsu ba sun tsere da raunukan harbin bindiga a farmakin da aka kai musu na baya bayan nan. Ya ce sojojin sun kwato shanu 57, wadanda yan bindigar suka sace, da kayan sojoji, da kayan bacci da tsabar kudi Naira dubu dari tara daga hannun ‘yan ta’addar.