Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ribas, Emeka Beke, ya yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, da ya janye matakin da kwamitin ayyuka na kasa ya dauka na rusa shugabannin jam’iyyar a jihar.
Beke, yayin da yake magana a Fatakwal a jiya, ya ce wa’adin shugabancin jam’iyyar a jihar bai cika ba.
Idan za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne kwamittin ayyuka na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Ganduje a Abuja, ya sanar da rusa shubannin kwamittin jami’iyyar a jihar Rivers tare da maye gurbinsa da ‘yan kwamitin riko wadanda zasu tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar na tsawon watanni shida. Shugaban kwamitin rikon, Cif Tony Okocha, wanda sanannen aminin tsohon gwamna Nyesom Wike ne na jam’iyyar PDP, wanda a yanzu yake kawance da jam’iyyar APC a matakin kasa.