Tinubu ya gaji matsalolin tabarbarewa tattalin arziki ne daga tsohuwar gwamnati – Charles Soludo

0 148

Gwamnan jihar Anambra Farfesa Charles Soludo, ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya gaji matsalolin tabarbarewa tattalin arziki ne daga tsohuwar gwamnatin da ya gada.

Soludo ya bayyana hakan ne a jiya yayin da yake tsokaci kan manufofin babban bankin Najeriya CBN a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels ta cikin shirin Politics Today.

Soludo, yayin da yake bayyana irin rawar da ya taka wajen dakile tsarin hada-hadar kudi a lokacin da ya jagoranci babban bankin kasar tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009, ya zargi CBN da buga kudi ba bisa ka’ida ba. Ya ci gaba da cewa, CBN ya gaza bin dokar CBN ta shekarar 2007, inda ya kara da cewa tun farko ana iya kaucewa tsarin matsalolin hada-hadar kudi a kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: