Gwamnatin shugaba Tinubu na da burin yin garambawul mai dorewa a fannin kiwon lafiya

0 129

Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ta amince da shirin sake fasalin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da na manyan cibiyoyi dubu 17,000 da 774 a fadin kasar nan baki daya.

Wannan dai na kunshe cikin wani jawabi da karamin ministan lafiya da walwalar jama’a, na kasa Farfesa Ali Pate, ya gabatar yayin zaman majalisar tattalin arziki kasa a jiya alhamis.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi karin bayani kan dabarun gwamnati lokacin da yake ganawa da ‘yan jaridu a fadar gwamnati jim kadan bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 137 wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Bala Muhammad ya koka da irin kididdigar da ke nuna tabarbarewar harkokin kiwon lafiya, ciki har da adadin mace-macen mata masu juna biyu da mutuwar jarirai.

Ya kara da cewa gwamnatin shugaba Tinubu na da burin kafa hadin gwiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki domin yin garambawul mai dorewa a fannin kiwon lafiya. Tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja ya kuma bayyana cewa akwa shirye-shirye da kwararru da masana kiwon lafiya domin cike gibin da aka samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: