Dalibai biyu na Jami’ar Tarayya ta Wukari da aka sace sun sami ‘yanci

0 134

Shugabar sashen yada labarai ta jami’ar, Mrs Ashu Agbu, ce ta bayyana hakan a cikin sakon WhatsApp da ta aike wa wakilinmu a yau Juma’a.

Sai dai ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda aka sako daliban ba.

An sace daliban biyu ne a ranar Laraba 3 ga watan Afrilu da misalin karfe 10:00 na dare a wani shago da ke kusa da makarantar. Daliban, Joshua Sardauna na Sashen Tattalin Arziki da kuma Obianu Elizabeth sun koma makarantar ne domin sake zana jarabawar da suka yi a sanadaiyar faduwa a wasdu kwasa-kwasai a lokacin da lamarin ya faru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: