‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida kuma wakilin gidan talabijin na Channels

0 151

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida kuma wakilin gidan talabijin na Channels, Joshua Rogers, a gidansa da ke Rumuosi a karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar Ribas a daren jiya Alhamis.

Rogers wanda ke aiki a gidan gwamnatin jihar Ribas, rahotanni sun ce an bi sawun sa ne bayan ya fito daga aiki zuwa gidansa.

Barayin sun tare shi kafin ya sauko daga motarsa, inda suka nuna masa bindiga da misalin karfe tara na dare. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanata ta ce tun da farko dan jaridar ya ba da labarin wani taron da aka yi a Ndoni a karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni na jihar inda Gwamna Siminalayi Fubara, ya kaddamar da wata cibiyar kula da lafiya a matakin farko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: