Dalibin aji biyar a ABU ya shiga hannu kan zargin lalata da kuma kisan wani mai shekaru 17

0 278

Wani dalibin aji biyar a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya (ABU) ya shiga hannu kan zargin lalata da kuma kisan wani dan sakandare mai shekaru 17 a Jihar Bauchi.

Dalibin jami’ar wanda ke karatun a fannin likitancin dabbobi ya fada komar Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ne bayan an tsinci gawar dan sakandaren a yashe a gefen titin wajen gari a Karamar Hukumar Misali ta Jihar Bauchi.

Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya na jihar, Ilelaboye Oyejide, ya ce bayan tsintar gawar a yashe cikin farin kyalle, “aka kai ta Babban Asibitin Misau, likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa, sannan aka gawar ga iyayensa suka yi masa jana’iza.

Kwamandan Hukumar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a yayin da ake masa tambayoyi, kuma a bisa hakan za a gurfanar da shi a kotu.

Oyejide ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa dan sakandaren ne zaro wuka ya yiwo kansa da ita, suka yi ta kokawa, inda a garin kare kansa ya soka wa marigayin wukar da ta yi ajalinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: