Emmanuel Macron ya ziyarci Tel Aviv domin tattaunawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

0 233

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Tel Aviv yau Talata domin tattaunawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

Ziyarar tasa na zuwa ne sama da makonni biyu bayan mayakan Hamas sun kutsa kai cikin Isra’ila daga zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe akalla mutane 1,400, galibi fararen hula da aka harbe, ko kuma aka kona su a ranar farko ta harin, a cewar jami’an Isra’ila daga cikinsu akwai ‘yan kasar Faransa 30.

A na sa ran Macron zai matsa kaimi wajen ganin an kawo karshen rikicin na Gaza.

Isra’ila ta ce an kashe mayakan Hamas kusan 1,500 a fafatawar da suka yi kafin sojojinta su sake kwace iko da yankin da ake kai wa hari.

Sama da Falasdinawa 5,000, galibi fararen hula ne aka kashe a zirin Gaza, a hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke kaiwa a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren kungiyar masu fafutukar Islama ta Falasdinu, bisa kididdigar da ma’aikatar lafiya ta Hamas ta bayar a Gaza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: