Za’a dauki masu NCE 50 karkashin shirin J-Teach a karamar hukumar Guri

0 512

Karamar hakumar Guri zata bullo da wani shirin koyarwa na wucin gadi wato J- Teach, domin daukar matasa 50 da suka kammala karatun NCE zuwa makarantun firamare.

Shugaban karamar hakumar Hon Musa Shaaibu Muhammed Guri ya bayyana haka lokacin da yake karbar bakuncin matasa masu shaidar kammala karatun NCE wanda suka kai masa ziyar har ofishin sa.

Musa Shaaibu Muhammed Guri yace karamar kaumar ta yanke shawarar bullo da shirn ne domin magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa. Haka kuma, ya kara da cewa, tsahohuwar gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin Alh Muhammed Badaru Abubakar ta bullo da shirin a 2018 inda aka dauki sama da mutane dubu a makarantun firamare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: