Amurka da Saudiyya za su ci gaba da tattaunawa da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan

0 244

Amurka da Saudiyya sun ce za su ci gaba da tattaunawa a Jeddah, da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan.

Rahotanni sun ce wakilan sojojin ƙasar Sudan da dakarun kar ta kwana na RSF sun isa birnin tashar jiragen ruwa na Saudiyya domin tattaunawa.

Tattaunawar zaman lafiya da ta gabata a birnin Jeddah ta ruguje a cikin watan Yuni bayan ƙeta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da dama.

A wannan karon an fahimci cewa, yunkurin shiga tsakani zai hada da mai gudanarwa na Afirka, daga ƙungiyar raya yankin Igad.

Rikicin watanni shida tsakanin sojojin Sudan da RSF ya haifar da bala’in jin kai.

Sama da mutane 9,000 ne aka kashe sannan wasu kimanin miliyan shida suka rasa muhallansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: