Majalisar dattijai ta nemi a kawo karshen matsalar ambaliyar ruwar da ke faruwa a fadin kasar nan

0 154

Majalisar dattijai ta bukaci gwamnatin tarayya ta kira taron masu ruwa da tsaki domin yin a kawo karshen matsalar ambaliyar ruwar da ke faruwa a fadin kasar nan.

Kudurin majalisar ya biyo bayan wani tsari ne da Sanata Adetokunbo Abiru daga jam’iyyar APC a Lagos ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Talata.

Babban zauren majalisar ya kuma jajantawa wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su tare da yabawa gwamnatocin Legas da Ogun bisa yadda suka shawo kan rikicin da bala’in ya afku.

Haka kuma ta umarci kwamitocin majalisar dattijai da abin ya shafa da su samar da isassun kudade ga hukumar NIMET don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Da yake gabatar da kudirin, Abiru ya ce, wasu al’ummomi da ke kusa da layukan gabar teku a Ikosi-Isheri da Agboyi-Ketu a Legas da sauran al’ummomi a Ogun sukan fuskanci ambaliyar ruwa a duk lokacin da aka bude madatsar ruwan Oyan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: