Gwamnatin jihar Binuwai ta ce an kammala shirye-shiryen fara samar da nau’in barasa a jihar

0 85

Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari da Kaddarori na Binuwai, Dr Raymond Asemakaha, wanda ya zagaya da ‘yan jarida a rangadin da ake shirin yi na samar da masana’antar barasa da ruwa da kuma biredi a garin Makurdi, ya ce shirin kafa masana’antar ta barasa ya zo ne a sakamakon nazari da aka yi a baya-bayan nan. wanda ya nuna makudan kudade da ke barin jihar duk wata akan shan barasa.

A cewarsa, binciken ya nuna cewa ana shan barasar da darajarsu ta kai Naira Milyan 870 duk wata a jihar Binuwai, yayin da a watan Disamba mazauna garin suka kashe sama da Naira Bilyan 1 wajen sayen barasa.

Asemakaha ya ce kamfanin na shirin baiwa ‘yan Binuwai da ‘yan Najeriya babban barasa da aka yi daga jihar, ta hanyar amfani da albarkatun kasa.

A yayin da yake bayyana cewa za a samar da danyen kayan a cikin gida, Asemakaha ya kara da cewa, kamfanin zai fara samar da shi gaba daya nan da makon farko na watan Disamba kuma aikin zai ci kudi tsakanin Naira Milyan 700m zuwa Naira Milyan 800.

Leave a Reply

%d bloggers like this: