An fara rangadin tantance kananan hukumomin da suka shafe kusan shekaru 10 babu wutar lantarki

0 178

Gwamnatin tarayya ta fara rangadin tantance kananan hukumomi takwas na shiyyar Sanatan Sakkwato ta Gabas da suka shafe kusan shekaru goma babu wutar lantarki da nufin maido musu da wutar lantarki.

Tawagar Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Daraktan Rarraba Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya, Mustafa Baba Umarah, a ranar Lahadin da ta gabata, ta ce tawagar da za ta tantance za ta yi nazari sosai kan matsalolin a cikin al’ummomin da abin ya shafa tare da mika rahoto ga Gwamnatin Tarayya.

A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar makamashi ta jihar Sokoto, Sanusi Dan Fulani, ya bayyana cewa an yi hakan ne domin a fara samun bayanai kan yanayi da kuma girman matsalar da ta kai ga baki daya a kananan hukumomi takwas na jihar.

A cewarsa, shirin maido da wutar lantarki ga al’ummomin da abin ya shafa, na daga cikin kokarin da gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ke yi na bunkasa harkokin tattalin arziki musamman mazauna karkara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: