Gwamnan jihar Kano ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano

0 107

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar tana ganin ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu matsalolin kiwon lafiya kamar sikila, cutar kanjamau, da ciwon hanta.

Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure a jihar Kano ba, ba tare da bada takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka.

Wannan shiri dai ya yi dai-dai da kudurin gwamnan jihar na inganta samar da yanayi mai kyau ga bangaren kiwon lafiya, da nufin ganin jihar Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadi.

Har ila yau, ya haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen da ke zaune tare da  masu HIV/AIDS, sickle cell anemia, hepatitis, da sauran su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: