‘Yan bindiga sun kai hari a unguwar Nasarawa da ke garin Maru a jihar Zamfara.

0 274

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Nasarawa da ke garin Maru, hedikwatar karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Da sanyin safiyar yau Juma’a ne maharan da yawa dauke da makamai suka mamaye yankin inda suka yi ta harbe-harbe don tsoratarda mazauna yankin.

Hukumomin ‘yan sanda a jihar har yanzu ba su tabbatar da sabon harin ba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara Yazid Abubakar bai amsa kiran wayar da gidan talabijin na Channels ya yi masa ba.

Sai dai wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa Dakarun Operation Hadarin Daji sun yi gaggawar amsa kiran da suka yi da ‘yan ta’addan a wata babbar musayar wuta da aka kwashe sama da awanni biyu ana yi.

Da yake lura da cewa babu tabbacin ko an sace wani mazaunin garin yayin harin, ya ce an kashe mutane uku ciki har da wani tsoho mai suna Mallam Isah.

A farkon wannan shekarar ma an kashe jami’in ‘yan sanda reshen karamar hukumar Maru da wasu jami’an ‘yan sanda biyu yayin da suka dakile wani harin makamancin haka da aka kai a hedikwatar karamar hukumar. Jihohin Arewa maso Yamma da sun kwashe shekaru suna fuskantar ta’addanci daga wasu gungun ‘yan bindiga, wadanda ke kai farmaki kauyuka suna kashewa tare da sace jama’a domin neman kudin fansa a yankunan karkara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: