Dalilan da yasa kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar ba da belin shahararren dan sanda Abba Kyari

0 104

Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar ba da belin shahararren dan sanda, Abba Kyari wanda ake zargi da safarar hodar Iblis.

Kotun ta yi watsi da bukatar ce a yau Litinin, a yayin sauraron shari’ar da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta shigar tana zargin Abba Kyari da wasu hafsoshin ’yan sanda shida kan safarar kwayoyin.

Zaman kotun ya gudana ne kimanin mako guda bayan Gwamnatin Tarayya ta amince ta mika Abba Kyari ga gwamnatin Amurka domin ya fuskanci wata shari’a a Kasar.

Abba Kyari na fuskantar zargin yana da hannu a wata damfara ta Dala miliyan 1.1 a Badakalar Hushpuppi, wanda ake zargin dan sandan da taimakawa wajen yin cutar da kuma tura kudaden da aka yi damfarar.

A lokacin zaman kotun da ke Abuja a yau, ta ce nan gaba za ta duba bukatar da Lauyoyin Abba Kyari suka gabatar mata na bayar da belinsa.

Da yake bayani bayan zaman kotun, lauyansa, ya bayyana cewa kotun za ta ci gaba da zaman sauraron sharia’ar a ranar 14 ga watan Maris da muke ciki.

Sai dai bai ce komai game da zaman kotun ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: