Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya ce mata sun fi maza kwarin Gwiwa a siyasa

0 127

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce mata sun fi maza kwarin Gwiwa, kuma basu da almundahana kamar yan’uwansu maza.

Da yake jawabi yayin wani taro da gidan talabijin na Channels ya shirya a jiya, Obi ya yi alkawarin kawo mata da yawa cikin gwamnati idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya tuno da yadda ya nada mata manyan mukamai a tsawon shekaru 8 da ya yi a jihar.

Shugaban jam’iyyar Labour kuma dan takarar kujerar shugbaan kasa a jam’iyyar ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta kunshi mata da matasa ne saboda suna fama da yunwa don kawo sauyi a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: