Danyan man da aka gano a yankin Neja Delta mallakin Najeriya ne bisa tanadin kudin tsarin mulki – Obasanjo

0 106

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa man da aka gano a yankin Neja Delta mallakin Najeriya ne bisa tanadin kudin tsarin mulkin kasarnan.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da dattijon Neja Delta, Cif Edwin Clark ya yi a wata budaddiyar wasikar da ya fitar kimanin mako guda da ya gabata.

A wata wasika mai shafi shida, Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa an zarge shi bisa kuskure.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa an yi kuskuren fahimtar kalaman da ya yi kan wannan batu a wani taro da wata gidauniya ta shirya a Abuja.

A ranar Laraba ne Clark ya caccaki Obasanjo kan abin da ya kira nuna rashin jin dadi da nuna kyama ga al’ummar jihohin da ake hako mai a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: