Dole sai an zakulo waɗanda suka kashe mana jami’an mu – Taoreed Lagbaja

0 147

Shugaban hafsan sojojin ƙasa Taoreed Lagbaja, ya ce dole sai an zakulo waɗanda suka kashe jami’ansu.

Rundunar sojin ta kuma zargi al’ummar yankin Okuama da ke jihar Delta da ya kasance wurin da aka kashe sojojinsu, da cewa sun koma farfaganda maimakon tsayawa a yi bincike.

Sojojin sun ce kisan da aka yi wa jami’nsu a jihar ta Delta abu ne da aka shirya shi.

Wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na sojojin, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce maimakon al’umman yankin su taimaka wa sojoji da bayanai da za su kai ga kama waɗanda suka kashe jami’ansu, sun koma yaɗa fargagandar karya da wofi.

Onyeama ya ce abin da suke yi ya nuna cewa kisan sojojin da aka yi wani abu ne da aka shirya tun farko kan dakarun.

Sojoji 16 ne ake zargin wasu matasa sun kashe a jihar ta Delta.

Manjo-Janar Onyeama Nwachukwu ya ce babu wata farfaganda da za ta hana kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Don haka, Onyeama ya buƙaci al’umma da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba, inda ya tabbatar musu da cewa babu wani harin ramuwar gayya da sojoji za su kai wa al’ummomin yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: