Wani dan kunar bakin wake ya mutu tare da jikkata mutum biyu a karamar a jihar Borno

0 197

Rundinar ‘yan sanda a jihar Borno ta tabbatar ta mutuwar wani dan kunar bakin wake tare da jikkata mutum biyu.

Kakakin rundinar ASP Daso Nuhum ne ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin.

Ya ce dan kunar bakin waken ya kashe kansa ne a lokacin da ya yi yunkurin kutsawa cikin masallata a lokacin da suke tsaka da sallar Tarawihi da misalin karfe 8 na daren jiya a cikin garin Biu, inda ya jikkata mutane biyu. Rundinar ‘yan sandan jihar ta yi kira ga jama’a da su kara sanya ido musamman cikin wannan wata na azumin Ramadana da al’ummar musulmi ke fita sallar dare tare da sanar da hukumomin tsaro da zarar sun ga wani abu da basu aminta da shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: